Tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya janye aniyarsa ta kafa kungiyar HISBA FISABILLALAHI mai zaman kanta a jihar Kano.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jigo a Jami’yar APCn Kano Dr. Baffa Babba Dan Agundi wanda ya fitar kuma ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa janye yunkurin ya biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano, wanda aka gudanar a ofishin yakin neman zaben Tinubu.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-haramta-samar-da-hisba-mai-zamanta-kanta-a-jihar/
Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne bayan kokawa da martanin jama’a da suka biyo bayan yunkurin kafa Hisbah mai zaman kanta, tare da shiga tsakanin da manyan masu ruwa da tsaki sukayi musamman gwamnatin Jihar Kano,da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/mun-samar-da-hisba-gandujiyya-ba-don-fito-na-fito-da-gwamnati-baza-mu-kaiwa-gwamna-ziyara-domin-neman-albarka-sheikh-ibn-si
A cewar sanarwar, taron ya yanke shawarar dakatar da kafa Hisbah Fisabilillah mai zaman kanta, ya faru ne domin bai wa Gwamnatin Jihar Kano damar duba batun sallamar yan Hisba da akayi tare da warware shi ta hanyar sulhu da fahimta.
Har ila yau, sanarwar ta jaddada girmama halattacciyar hukumar Hisba da ake da ita , tare da kudurin ba da cikakken hadin kai ga hukumomin tsaro wajen tabbatar da doka da oda, da kuma tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar Kano da kasa baki daya.
TST Hausa ta rawaito cewa batun kafa Hisba FISABILLALAHI din ya tada kura a Kano.

