Hukumar Kula da ganin wata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal na shakerar 2026 a ƙasar ba.
Hakan na nufin za a azumci ranar Alhamis 19 ga watan Maris na shekarar 2026 daidai da 30 ga watan Ramadan 1447 bayan Hijra inda a bana za’a gabatar da azumi guda 30 kenan.
Don haka ranar Juma’a 20 ga watan Maris na shekarar 2026 itace ta kasance ranar Sallah karama.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/baa-ga-watan-mauludi-a-najeriya-ba-sarkin-musulmi/
Shafin sada zumunta na Haramain ya rawaito cewa kwarraru masu binciken ganin wata 25 ne suka zauna duba jaririn watan na Shawwal,amma ba’a ganshi ba.
TST Hausa ta rawaito cewa ,dama tuni masana kimiyar taurari da sararin samaniya suka shaida cewa azumin na bana 30 za’a yi maimakon 29 saboda wasu dalilai na kimiyar taurari da kuma yadda gajimare ya rufe sararin samaniyar kasar.
Anga yadda gajimare ya rufe yammacin kasar ta Saudiyya,Inda ya kamata ace anga watan na Shawwal.
Ko a shekarar 2025 ma haka ta kasance inda aka cika azumi 30 bayan gaza ganin watan na Shawwal.

