Wasu ’yan ta’adda sun sauya wuraren buya da sansanonin da suke amfani da su bayan hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai a wasu yankuna da ake zargin suna amfani da su a matsayin mafaka.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun nuna cewa hare-haren sun tarwatsa muhimman wuraren da ’yan ta’addan ke gudanar da ayyukansu, lamarin da ya tilasta musu barin wuraren tare da komawa wasu yankuna domin gujewa karin farmaki.
Majiyoyin sun bayyana cewa duk da cewa hare-haren sun rage karfin ’yan ta’addan,da sauya wuri ba yana nufin an kawar da barazanar gaba daya ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/muna-bukatar-tinubu-ya-yiwa-yan-kasa-bayani-na-gamsarwa-kan-harin-amurika-a-najeriya-sakon-pdp-ga-tinubu/
Sun jaddada bukatar ci gaba da tattara bayanan sirri da hada kai tsakanin hukumomin tsaro na cikin gida da na kasashen waje domin hana ’yan ta’addan sake hada kai ko kai wasu hare-hare.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kwan-kaji-yayi-tashin-goron-zabi-a-kasata-kuma-joe-biden-keda-hannu-inji-trump/
Masana harkokin tsaro sun kuma gargadi cewa irin wannan sauya matsuguni na iya zama wata dabara ta ’yan ta’adda don tserewa matsin lamba, suna mai kira ga gwamnatoci da su kara sa ido da tsaurara matakan tsaro a yankunan da ake zargin sun koma.

