Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce ba daidai ba ne yadda wasu ’yan Najeriya ke kallon ’yan majalisar dokoki a matsayin mutane da ke zuwa Majalisa domin tara kuɗi kawai.
Akpabio ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yi wa Majalisar Tarayya, inda wasu ke zargin ’yan majalisa da zama ’yan amshin shata maimakon wakilan al’umma.
Ya jaddada cewa rawar da majalisar dokoki ke takawa ta wuce hakan, yana mai cewa aikinsu shi ne wakiltar jama’a, tsara dokoki nagari, da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati domin amfanin ƙasa baki ɗaya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ina-rokon-dss-da-ofishin-nsa-su-binciki-masu-cewa-na-mutu-akpabio/
Shugaban majalisar ya ƙara da cewa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin bangaren majalisa da bangaren zartarwa na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci zaman Majalisar Tarayya domin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026, inda ya buƙaci ’yan majalisa su ci gaba da bayar da gudunmawa ta hanyar goyon bayan manufofin da za su amfani al’umma

