Masana harkar abinci a Najeriya sun bayyana damuwa kan yawaitar amfani da mai da ba shi da sunan kamfani kuma ba a masa fortifikashan, suna mai jan hankali cewa wannan dabi’a na barazana ga lafiyar jama’a, musamman yara da masu rauni.
Wannan batu ya fito fili ne yayin wani taron bita na kwana guda da aka shirya wa editocin lafiya na kafafen yada labarai, wanda Gidauniyar Global Alliance for Improved Nutrition (GAIN) tare da haɗin gwiwar CS-SUNN, SNO da e-HEALTH Africa suka shirya, a Tahir Guest Palace, Kano.
Bisa ga bayanan da Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ta fitar, kimanin kashi 67% na ‘yan Najeriya ne ke amfani da mai mara suna kuma ba shi da fortifikashan, yayin da kashi 31% kacal na man girki da ake sayarwa a kasuwa ne aka yi masa fortifikashan.
Wannan al’amari na haifar da gibi mai girma a fannin abinci mai gina jiki, wanda ke haddasa karancin sinadirai kamar Vitamin A.
Hope Ikani, jami’ar shirin CS-SUNN, ta bayyana cewa amfani da man da ba a yi wa fortifikashan ba duk da cewa farashinsa ya fi sauki yana da illa mai tsanani a dogon lokaci ga lafiyar jama’a.
Ta ce an sami gagarumin ci gaba wajen rage yawan yaran da ke fama da karancin Vitamin A da suka haura miliyan uku, ta hanyar shirin fortifikashan, amma yawaitar sayen mai mara suna a kasuwa na barazana ga wadannan nasarori.
Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun bukaci jama’a da su guji amfani da irin wadannan man da ake sayarwa a kasuwanni ba tare da tantancewa ba, inda suka bayyana cewa ba su da sinadaran gina jiki kuma galibi ana hada su da wasu abubuwa masu illa.
Peter Olushola, mai kula da sashen sadarwa na CS-SUNN, ya jaddada bukatar sanya shirin fortifikashan a matsayin wani bangare na tsarin kiwon lafiya na kasa tare da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
Daga cikin muhimman shawarwarin da aka tattauna a taron sun hada da:
Dokar tilasta fortifikashan: kafa dokoki da za su tilasta kamfanoni yin fortifikashan ga kayan abinci.
Inganta tsari da sa ido: hukumomin da ke da alhaki su karfafa sa ido don tabbatar da samuwar abinci mai gina jiki a kasuwa.
Hadin gwiwar kafafen yada labarai: ‘yan jarida su rika kawo rahotanni masu gamsarwa da hujjoji domin fadakar da jama’a da karfafa daukar mataki.
Masana sun bayyana cewa fortifikashan a matakin kasa ba kawai shiri ne na kiwon lafiya ba, har ila yau wata dabarar ci gaban kasa ce wadda ke taimakawa wajen bunkasa kwakwalwar yara, rage kudin kula da lafiya da kuma habaka tattalin arziki.
Taron ya bayyana bukatar hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban da kuma kafafen yada labarai domin karfafa kokarin Najeriya na inganta abinci, da kare lafiyar yara da mabukata a cikin al’umma.

