Yan jarida mata guda biyu sun ajiye aikinsu a Gidan Rediyon Amasco FM da ke Jihar Kano,bisa Radin Kansu.
Yan Jaridar sun hada da Halima Abdullahi da ta kasance shugabar Sashen Labarai na Amasco Radiyo da Hidiya Salisu Ahamad mataimakiyar shugaban Sashen Labarai.
Wata Majiya daga gidan Radiyo na Amasco din da ta nemi a boye sunanta ta shaidawa TST Hausa cewa ’yan jaridar sun ajiye aikinsu ne a bisa radin kansu duk da cewa har yanzu ba su bayyana dalilansu na yin hakan ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kalma-daya-ka%c9%97ai-na-iya-tayarda-hankali-a-labaranku-na-internet-farfesa-ibrahim-ya-gargadi-yan-jarida/
Majiyar ta shaida cewa ana rade radin ko zasu dogara da kansu ne a aikin na jarida,shiyasa suka dauki wannan matakin duk dacewa basu sanar da hakan a hukumance ba.
Wasu daga cikin ma’aikatan na Amasco FM sun bayyana cewa matakin ya sanya su cikin damuwa musamman ganin yadda aka jima ana aiki tare.

