‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wanda ya lashe gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar kwanan nan, Abdulsalam Rabi’u sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 30 kafin sakinsa.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar Talata ne ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da Rabi’u tare da mahaifinsa da ‘yan uwansa a kusa da Labin Bangori a jihar Katsina.
Rabi’u dan asalin jihar Katsina kuma dalibin likitanci a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya zama zakara a gasar Hizifi 60 tare da Tajweed a musabukar da aka gudanar a jihar Kebbi.
An yi garkuwa da shi ne bayanda gwamna Dikko Umar Radda na katsina ya gayyaci shi da mahaifinsa zuwa gidan gwamnati domin karramashi tare da bashi kyaututtuka.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun dauke Rabi’u ne tare da mahaifinsa da kuma wasu ‘yan uwansa yayin da suke komawa gida bayan bikin karramashi.
A yanzu haka kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Katsina, Bala Salisu-Zango a wata hira da aka yi da shi ya tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya su naira miliyan 30.
Ya kara dacewa gwamnan jihar ya kadu matuka da samun labarin sace dalibin shida iyayensa.

