Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jaridu na Najeriya (NUJ), Comrade Alhassan Yahaya, tare da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, sun kaddamar da ofishin kungiyar yan Jaridu masu Wallafa labarai a yanar gizo wato Kano Online Media Chapel a cikin bukukuwan Kano makon yan jarida na 2025.
Kwamared Yahaya ya bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin NUJ na ƙarfafa aikin jarida,da inganta yanayin ma’aikatan jarida, da kare hakkokinsu.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/labarin-dan-jaridar-da-ya-kafa-tarihi-a-duniyar-yada-labarai-a-kafar-sadarwa-ta-zamani/
A jawabinsa,Kwamared Waiya ya tabbatar da cewa gwmanatin Jihar Kano za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ‘yan jarida domin samar da sahihan bayanai ga jama’a.
Shugaban kungiyar ta Kano Online Media Chapel,Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya godewa NUJ da gwamnatin jihar kan goyon bayan da aka ba su, inda ya jaddada cewa za su yi aiki bisa ƙa’idoji da ɗabi’a wajen inganta labarai masu sahihanci.

