Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, yaci Alwashin kawo karshen matsalar tsaro da ta fara addabar wasu yankuna na kananan hukumomin jihar.
Gwamnan ya shaida hakan ne a garin Dan Kamaye dake karamar hukumar Tsanyawa lokacin da ya jagoranci tawaga mai karfi da ta hada da jami’an sojojin sama da na kasa da Yan Sanda da DSS domin rangadin yankunan da yan bindiga suka kai hare hare a Tsanyawa da Shanono.
Gwamnan, ya ce matakin ya biyo bayan rahotannin matsalolin tsaro da suka nuna cewa wasu bata-gari na ƙoƙarin samun hanyar kutsa kai cikin jihar ta kananan hanyoyi dake iyaka da Katsina.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kano-na-zaune-lafiya-ina-rokon-jamaa-su-daina-bari-ana-razana-su-gwamna-yusuf/
Ya ce an kammala nazari tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro, inda aka gano wasu wurare da ke buƙatar daukar matakan gaggawa akan sha’anin tsaro.
Gwamna Yusuf ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da inganta tsaro ta hanyar kafa karin wuraren duba motoci , da kuma karfafa hukumomin tsaron jihar.
Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai da hukumomin tsaro ta hanyar sanar da duk wani motsi ko mutum da suke zargi.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-magantu-kan-zargin-dawowar-sanaar-achaba-a-birnin-kano-da-kewaye/
Gwamnan ya tabbatar da cewa Kano da Katsina jihohi ne dake makotaka da juna kuma sun jima suna cikin zumunci da zama lafiya,a dan haka ya nemi mutanan Katsina da su rika bada bayanan sirri ga jami’an tsaro duk lokacin da yan bindigar jihar suka nufo Kano.
Yace sulhun da akayi da yan Bindiga a Katsina shine ya janyo suke shigowa Kano suna satar mutane

