Kungiyar tsoffin ɗalibai na makarantar share fagen shiga jami’a, CAS Kano, aji na 2002, sun rabawa marayun da abokan karatunsu suka mutu suka bari kuɗi naira miliyan 2 da dubu dari 780.
Wannan na a matsayin wani yunƙuri na taimako da jin-ƙai ga iyalan abokan karatu da su ka rasu.
An yi rabon tallafin ne ga marayun, 73, a harabar makarantar ta CAS inda hakan ya haifar da koke-koke da zubar da hawaye daga wasu ƴan ƙungiyar da su ka halarci taron saboda tausayawa.
Babban abinda ya janyo zubar da hawaye shine yadda yan Kungiyar,suka fahimci cewa ,kayan sallar da suka bayar da kuɗi,ya janyo sanya farin ciki a zukatan marayun da iyayensu.
Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin walwala na ƙungiyar, Mansur Tukur Hotoro, yace ƴan kungiyar ne su ka tara kuɗin har naira miliyan 2,600,000 a cikin wata daya.
A cewar sa, bayan an yi lissafi da yawan marayun da kuma adadin kuɗin da za a baiwa kowanne, sai kungiyar ta cika naira dubu 180 daga asusun ta domin adadin ya kai yadda ake so.
Ya ce duk mamata masu ƴaƴa ɗai-ɗai an baiwa marayun su naira dubu 50, masu biyu-biyu an basu Naira dubu 40, masu uku-uku kuma an baiwa kowanne Naira dubu 35 da sauran su.
“Mun fara wannan tallafi ne a bara, 2024 domin tunawa da taimakon iyalan abokan karatun mu da su ka riga mu gidan gaskiya.
“Mun ci alwashin ɗorewa da wannan tallafi har bayan ran mu. Ina kira ga iyayen da aka barwa marayun nan da su rike su da kyau kamar yadda Addinin Musulunci ya yi horo da kulawa da maraya”; Inji shi.
“Mu na addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya kyauta makwanci, mu kuma Allah Ya kyauta namu zuwan,” in ji Hotoro.

