Gwamnatin shugaba Tinubu zata sake ciwo sabon bashin kudi naira Tiriliyan 17 da doriya a shekarar 2026 domin cike gibin kasafin kuɗin shekarar sakamakon ƙalubalen samun kuɗaɗen shiga idan aka kwatanta da yawan kuɗin da ake bukatar kashewa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/duk-wanda-ya-yarda-zai-bar-amurika-ya-koma-kasarsa-zamu-bashi-kyautar-dala-1000-inji-trump/
Wannan na kunshe ne a tsarin kasafin kuɗin 2026 da aka fitar daga Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, wanda ya nuna cewa adadin bashin da za a ciwo zai karu kan wanda aka ciwo na naira Tiriliyan 10 a shekarar 2025 zuwa sama da naira Tiriliyan 17 a sabuwar shekarar 2026.
Rahoton ya ce ƙaruwar bukatar aro kudin na da nasaba da fadada gibin kasafi da kuma raunin hasashen kuɗaɗen shiga, duk da cewa ana sa ran raguwar yawan kuɗin kashewa gabaɗaya idan aka kwatanta da shekarar da ake ciki.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-ya-warewa-mafi-karancin-albashin-maaikata-naira-biliyan-845-a-shekarar-2025/
A cewar takardar, gibin kasafin 2026 zai kai naira Tiriliyan 20 idan aka kwatanta da naira Tiriliyan 14 da aka amince da shi a kasafin 2025.
Rahoton ya kuma nuna cewa kuɗin da ake sa ran samu cikin kasafin tarayya banda na hukumomin gwamnati masu zaman kansu zai ragu daga naira Tiriliyan 38 a 2025 zuwa naira Tiriliyan 29 a 2026.

