Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan mummunan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Chiranci da ke Jihar Kano.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa rundunar ’Yan Sandan Najeriya bisa saurin kama waɗanda ake zargi, tare da bayar da umurnin a gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da su gaban shari’a domin su fuskanci hukunci.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/matashin-da-ya-jagoranci-taaddancin-dorayi-shine-ake-zargi-da-kone-mata-biyu-a-tudun-yola-in-ji-yan-sanda/
Tinubu ya bayyana kisan a matsayin aikin ta’addanci da rashin imani, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa.
A wata Sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanugan ya fitar ya kuma nuna alhininsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji (Dr.) Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen makon da ya gabata.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa rasuwar marigayin ba rashi ne kadai ga Jihar Kano ba, illa rashi ne ga ƙasar nan baki ɗaya, la’akari da irin rawar da ya taka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa kan ’yan kasuwa a faɗin Najeriya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/babu-dalilin-jin-tsoron-bata-gari-dan-sun-rike-wuka-kwamanda-shehu-ya-gargadi-masu-raguwar-zuciya/
Shugaban Ƙasa ya kuma yabawa gudunmawar da ya bayar a yaƙin neman zaɓen shekarar 2023, da jajircewarsa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kishin ƙasa ta hanyar Patriotic Elders Network for Peace (PENP) da ya kafa.
Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar ’yan kasuwa na Kano, jama’ar jihar, da kuma gwamnatin Jihar Kano bisa wannan babban rashi.

