Kungiyar yan kishin Najeriya,wato Nigeria patriotic front movement (NPFM) sun sake shirya zanga zangar lumana a sassan Najeriya daga ranar 1 ga watan Augusta na shekarar 2025.
A wani taron manema labarai da Kungiyar ta yan kishin Najeriya karkashin jagorancin shugabanta Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ta shirya a birnin Kano ta bayyyana wasu daga cikin dalilan sake komawa zanga zangar makamanciyar wacce suka shirya a ranar 1 ga watan Augusta na shekarar 2024.
Kwamared Abdulmajid yace zasu koma Zanga zangar ne domin tunawa da wadanda suka mutu ko suka bace a zanga-zangar da ta gudana a shekarar da ta gabata, da kuma sake jaddada bukatar kawo karshen mulkin rashin adalci da kuma tsadar rayuwa da ke gallaza wa ‘yan Najeriya.
Kungiyar yan kishin Najeriya sun ce a yayin zanga zangar zasu sake gabatar da Muhimman Abubuwan ga Shugaban kasa da suka hada :
1. Adalci ga waɗanda suka mutu ko suka bace a 2024
Kungiyar ta bukaci gwamnati ta yarda cewa ta kashe fararen hula da ba su da laifi, ta nemi gafara, sannan ta biya diyyar dangi da iyalan da abin ya shafa.
2. Gyara fannin tsaro:
Fiye da mutane 2,124 aka sace daga Janairu zuwa Yuli 2024, inda aka biya fiye da naira miliyan 389 a kudin fansa.
Jihohin da suka fi fuskantar matsalar sace mutane sun hada da Zamfara (667), Kaduna (454), da Neja (253).
Mutane 10,217 sun mutu cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Tinubu, a cewar Amnesty International.
‘Yan sanda da sojoji ba sa samun kayan aiki da albashi mai kyau duk da hadarin da ke tattare da aikinsu.
3. Saukin rayuwa da rage farashin kayayyaki.
Farashin abinci da mai sun yi tashin gwauron zabo, yayin da albashi da kudin shiga na mutane ya tsaya cik.
4. Kawowa da gaggawa ga cin hanci da rashawa.
Ana yi wa wasu rufa-rufa yayinda ake tursasawa wadanda ba sa goyon bayan gwamnati.
Kungiyar na bukatar a rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen biyan ‘yan siyasa.
5. Mayar da manyan kamfanonin gwamnati na zamani:
A dawo da NNPC, lantarki, da kamfanin sadarwa na NITEL hannun gwamnati don samar da ci gaban masana’antu da kare kasa.
6. Albashi mafi karanci na gaskiya:
A kai albashin mafi kankanta zuwa ₦250,000 a kowane wata.
A biya duka hakkokin yan fansho da kudin ritaya.
7. Dakatar da kwace gonakin talakawa:
Kungiyar ta zargi manyan masu rike da madafun iko da kwace filaye da gonaki, musamman a Arewacin Najeriya, lamarin da ke kara rikicin tsaro.
8. Ilmi na kowa da kowa:
A tabbatar da cewa kowa zai iya samun ilimi ba tare da biyan bashin karatu ba. A mayar da bashin karatu zuwa tallafi.
9. Dakatar da sabbin bashin kasashen waje
NPFM ta nuna damuwa da yadda bashin Najeriya ya haura dala biliyan 46 a 2025, duk da cewa an share duka bashin a zamanin Obasanjo.
Kungiyar ta zargi Shugaba Tinubu da kinkin kin sauraren koke-koken jama’a tun bayan zanga-zangar da aka yi a bara, inda ya zargi matasa da tada zaune tsaye maimakon daukar matakan rage tsadar rayuwa.
Ta kuma bayyana cewa jam’iyyar APC ta mamaye sauran jam’iyyun adawa, kuma hakan yana yi wa tsarin dimokuradiyya zagon kasa. Ta bayyana gwamnati a matsayin “Mai nuna karfi da iko ba tare da bin doka ba.”
Kira ga ‘Yan Najeriya:
NPFM ta jaddada cewa zata ci gaba da gwagwarmaya ta lumana duk da yiwuwar barazana ko farmakin jami’an tsaro.
Kungiyar ta jaddada cewa babu ci gaba da za a samu sai da shugabanni masu kishin kasa.

