Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa da tutocin Najeriya a ko ina cikin sassan Najeriya domin alhinin rasuwar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar,yace Shugaba Tinubu ya kuma bada umarni ga mataimakinsa Kashim Shettima da ya tafi birnin London domin Shirin dawo da gawar marigayi Buhari.
Sanarwar ta kara dacewa,tuni kafin nan Bola Tinubu ya kira uwar gidan Buhari Aisha Buhari ta wayar tarho ya nuna kaduwarsa da mutuwar marigayin.
Tinubu yace Najeriya tayi rashin jajirtaccen mutum kuma dan kishin kasa.
Ya rasu ne a yammacin Lahadi a London yana da shekaru 82 da haihuwa a duniya.
Ya rasu ya bar mace daya da ya ya guda 10 da jikoki da yan uwa.
Ya ya biyar ya same su ne da tsohuwar matarsa Hajiya Safinatu Yusuf,sai ya ya biyar da ya samesu da uwar gidansa ta yanzu Aisha Halilu.

