Majalisar zartaswa ta kasa ta amince a kashe naira miliyan dubu 80 domin sake gina madatsar ruwa ta Alau dake birnin Maiduguri a jihar Borno
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev ya bayyana haka a ranar Talata bayan kammala taron majalisar zartarwa na tarayya wanda shugaba Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Utsev ya ce, gwamnatin jihar Borno na hada kai da gwamnatin tarayya domin fara aikin da aka shirya gudanarwa cikin watanni 24 masu zuwa.
Ministan ya kuma shaida cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025.
Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Hakan ya biyo bayan Rahoton kwamatin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa akan ambaliyar ruwan da akayi a cikin birnin Maiduguri a watan Satumbar shekarar 2024.
An kafa kwamatin ne a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2024 ,mako daya bayan faruwar ambaliyar

