Babbar jami’ar Bankin mai kula da ayyuka a bankin na Duniya , Anna Bjerde, ta sanar da hakan inda ta ce ana yawan ambaton Najeriya a yanzu a sassan duniya a matsayin abar buga misali a bangaren iya shugabanci mai ɗorewa da sahihin sauye-sauyen tattalin arziki.
Ta faɗi hakan ne yayin wata ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-tuntu%c9%93e-ya-yi-wanda-zai-iya-fadawa-kan-kowaamma-ba-faduwa-ya-yi-ba-in-ji-fadar-shugaban-kasa/
Ministan Kuɗi kuma Ministan Daidaita Tattalin Arziki, Wale Edun, da Mataimakin Babban Ma’aikacin Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Hassan Hadejia, sun kasance tare da Shugaban Ƙasar wajen karɓar baƙuwar, yayin da Anna Bjerde ta samu rakiyar wasu manyan jami’an Bankin Duniya.
Babbar jami’ar ta yaba da irin sauye-sauyen da gwamnatin Najeriya ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata, tana mai cewa jajircewar gwamnati na ci gaba da tafiya kan turbar gyare-gyare duk da ƙalubale ya cancanci yabo.
Ta bayyana cewa daidaito da kuma alamun samun sakamako mai kyau da ake gani a fili sun ƙara gina kwarin gwiwa a zukatan masu zuba jari, masu tsara manufofi da kuma masu zaman kansu a fannin kasuwanci.
Tace a yanzu yan Najeriya na cikin Walwala fiye da baya kuma, ya nuna cewa Shugabancin Tinubu abin koyi ne.
Anna Bjerde ta ƙara da cewa sabon tsarin haɗin gwiwar Bankin Duniya da Najeriya ya ginu ne bisa hangen nesa da manufofin ci gaban ƙasar, musamman burin cimma tattalin arziki da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya tare da haɓakar tattalin arziki da kashi bakwai cikin ɗari.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yan-najeriya-basa-shayin-kashe-kudi-sunyi-amfani-da-fetur-na-naira-tiriliyan-1-58-a-bikin-kirsimeti-in-ji-gwamnatin-tinubu/
A nasa jawabin, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta ja da baya ba kan sauye-sauyen tattalin arziki da take aiwatarwa, duk da amincewa da cewa matakan sun kasance masu wahala a farko.
Ya ce cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗaɗe sun jawo hauhawar farashi da farko, amma daga baya hauhawar ta ragu sosai, yayin da kuɗin naira ya samu daidaito, lamarin da ya ƙara ƙarfafa gwiwar masu zuba jari tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci a ƙasar.

