Shugaban gidan Radiyon Hikima FM Kano, Malam Abubakar Isa Dandago ya ajiye aikinsa nan take.
Dandago wanda ya yi aiki da kafafen yada labarai da dama a jihar Kano yace a wannan yanayi na damuwa yana bakin cikin shaida cewa ya ajiye aikinsa ne bisa radin kansa.
MD Dandago, ya ajiye aikinsa daga mukaminsa,ne kwanaki kadan bayan shugaban sashen siyasa na gidan Malam Aliyu Sufiyanu ya ajiye aikinsa.
KARIN LABARAI :https://tsthausa.com/yan-jarida-mata-biyu-sun-ajiye-aiki-a-gidan-rediyon-amasco-fm-kano/
TST Hausa ta rawaito cewa haka kuma a makon nan ne mata biyu yan Jarida Halima Abdullahi da Hidiya Ahamad daga gidan Radiyon Amasco suka ajiye aikinsu.
Matakin da yan jaridar ke dauka na ajiye aikinsu na cigaba da jawo hankalin ma’aikatan kafafen yada labarai a Kano da masu sauraron gidan rediyon a jihar Kano.
Bayanai sun nuna cewa Malam MD Dandago ya sanar da ajiye aikin nasa ne a hukumance, sai dai zuwa yanzu ba a bayyana takamaiman dalilan da suka sa ya ɗauki wannan mataki ba.
Haka kuma shugabancin gidan rediyon bai fitar da wata sanarwa ta musamman da ke ƙarin bayani kan batun ba.
Wasu majiyoyi a cikin gidan rediyon sun ce matakin na iya kasancewa yana da alaƙa da sauye-sauye na shugabanci ko wasu dalilai na cikin gida, amma har yanzu babu tabbacin hakan daga ɓangaren da abin ya shafa.

