Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, zai zamo Malami na farko da zai fara gabatar da Tafsirin watan Ramadan na shekarar 1447 Hijiriyya a gobe Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026, a Masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadan-gwamnan-sokoto-aliyu-ya-bada-umarnin-fara-biyan-maaikatan-jihar-albashin-fabareru-nan-take/
Za a fara karatun ne bayan sallar La’asar, inda ake sa ran ɗimbin al’umma daga sassa daban-daban za su halarta domin sauraron darussan tafsiri da malamin ke gabatarwa duk shekara.
A sanarwar da malamin ya fitar a shafinda na Facebook da sauran shafukan sada zumunta ya ce masu sha’awar bibiyar tafsirin daga nesa kuma za su samu damar kallon karatun kai tsaye ta kafafen sada zumunta da suka haɗa da Facebook, YouTube da TikTok.
Haka kuma, an tanadi hanyar samun sautin karatun ta manhajar WhatsApp domin sauƙaƙa wa masu bukata.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/ramadangwamna-zulum-ya-dakatar-da-karbar-haraji-ga-yan-kasuwar-borno/
Masu shirya tafsirin sun bayyana godiyarsu ga waɗanda suka riga suka bayar da gudunmawa domin tallafawa ayyukan da ake gudanarwa, tare da kira ga sauran masu sha’awar bada tasu gudunmawar su bi hanyoyin da aka tanada.
Ana sa ran tafsirin zai gudana cikin tsari da natsuwa kamar yadda aka saba a kowace shekara, inda al’umma ke cin gajiyar darussa, nasihohi da bayanai kan al’amuran addini da zamantakewa.

