Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi Allah-wadai da lalata wasu daga cikin allunan talla da ke ɗauke da hoton Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
TST Hausa ta rawaito cewa wasu matasa sun lalata wasu daga cikin allunana tallan takarar gwamna Abba Kabir Yusuf a wurare daban-daban a cikin birnin Kano lokacin hawan da sarki Aminu yayi na Fatahu Yakasai.
Sarkin ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin da bai dace ba, tare da bayar da umarnin gaggauta maye gurbin dukkan allunan da aka lalata.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata a mutunta dukkanin alamu da kayayyakin da aka sanya a wuraren taruwar jama’a, tare da kauce wa duk wani mataki da ka iya haifar da tashin hankali ko rarrabuwar kai a tsakanin al’umma.
A cewar rahoton, Sarkin ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da mutunta juna tare da tabbatar da zaman lafiya, duk da bambance-bambancen ra’ayoyin siyasa.
An ce an fara aiwatar da umarnin maye gurbin allunan da aka lalata nan take.

