Tsohon dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu Sanata Kabiru Gaya ya jajanta wa al’ummar Jihar Kano da Gwamnatin Jihar Kano bisa mummunan iftila’in da ya afku na kisan gillar da aka yi wa wata matar Aure da yayanta shida
Kabiru Gaya ya bayyana, lamarin a matsayin abinda ya jefa al’umma cikin alhini da firgici.
Sanatan yace abinda ya faru rashin Imani ne da rashin tausayi inda ya ce wannan mugun aiki ya girgiza zukatan jama’a tare da lalata zaman lafiya da tsaron da Kano ta dade tana alfahari da shi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-ya-umarci-a-gaggauta-bincike-da-hukunta-wadanda-suka-kashe-matar-aure-da-yayanta-a-kano/
Ya yabawa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa gaggawar ɗaukar mataki da jajircewar da suka nuna wajen cafke waɗanda ake zargi da aikata laifin, yana mai kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi domin ganin an kamo duk sauran masu hannu a ciki.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/matashin-da-ya-jagoranci-taaddancin-dorayi-shine-ake-zargi-da-kone-mata-biyu-a-tudun-yola-in-ji-yan-sanda/
Sanata Kabiru Gaya ya buƙaci a tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa tanadin doka, domin ya zama izina ga masu aikata miyagun laifuka a nan gaba.
A ƙarshe, Sanatan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya sanya su a Aljannar Firdausi, tare da roƙon Allah Ya bai wa iyalansu da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi.

