A yayin da ake bikin ranar kare ’Yancin dan Adam ta duniya, shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta Najeriya Human right network Kwamared AA Haruna Ayagi, ya ce lokaci ya yi da za a duba ƙorafin maza da ke fuskantar takurawa daga matansu, musamman waɗanda ke hana mazajensu kara aure na biyu ko na uku zuwa mata ta hudu wanda hakan ya saba da tsarin addini da hakkin da mazan ke da shi.
A duk ranar 10 ga watan Disamba na kowacce shekara majalisar dinkin duniya ke bikin ranar kare hakkin Bil’adama ta duniya.
Ayagi, wanda ya yi jawabi a shirin Zaman Yan Marina na gidan Radiyo Rahma,Kano a wani bangare na bikin ranar kare hakkin dan Adama ta duniya ,ya bayyana cewa akwai ƙara yawaitar korafe-korafe daga maza da ke fuskantar matsin lamba, da barazana ko cin zarafi daga matansu saboda batun ƙarin aure.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/duk-da-na-cika-shekara-100-a-duniya-da-zaa-hada-min-dukiyar-najeriya-ina-so-tanko-yakasai/
Ya ce irin wannan takura na iya zama take hakki, wanda ya sabawa ’yancin dan Adam da tsarin shari’a.
TST Hausa ta rawaito cewa Kwamared AA Ayagi ya yi nuni da cewa hukumomi da al’umma su duba batun ta fuskar kare ’yancin mazaje da tabbatar da zaman lafiya a gidajen aure.
Ayagi ya kara da cewa manufar kalamansa ba domin haddasa rigima ba ce, sai dai don jan hankali kan muhimmancin mutunta ’yancin juna tsakanin ma’aurata musamman a rana irin ta kare hakkokin bil’adama.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/muna-tare-da-gwamnatin-kano-a-shirinta-na-kwashe-kananan-yara-daga-kan-tituna-inji-malamai/
Yace matsalar tafi kamari a wannan lokaci da yan Mata sukayi yawa a gari ga kuma bayyanar tarin Zaurawa ba mazan Aure,inda yace ya zama wajibi a duba lamarin.
Yace za su cigaba da hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin cigaba da kare yancin maza a Arewacin Najeriya domin tabbatar da adalci da sulhu.

