Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da dakatar da karɓar haraji na tsawon shekaru biyu daga hannun ƴan kasuwar jihar.
Gwamna Zulum ya janye harajin ne ga ƴan kasuwar da ambaliyar ruwa ta watan Satumbar shekarar 2024 da gobarar kasuwar Maiduguri Monday Market suka shafa.
Shugaban hukumar karɓar haraji ta jihar Borno Farfesa Ibrahim Bello, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka sanyawa hannu akan rabawa manema labarai a birnin Maiduguri.
Sanarwar tace an fara daukar matakin ne daga watan Ramadan domin samun saukin rayuwa.
Farfesa Ibrahim Bello ya ce wannan mataki na da nufin farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma ragewa ƴan kasuwa biyan kuɗaɗe kan kasuwancinsu.
Sannan gwamnatin ta Borno tace tana fatan yan kasuwar zasu amfana da wannan dama suma su saukakawa jama’a a wannan lokaci na azumin Ramadan da bayan watan.
Da wannan rangwamen harajin, Gwamna Zulum na fatan tallafawa ƴan kasuwa da iftila’i ya shafa, domin su sami damar farfaɗowa da zuba jari a kasuwancinsu ba tare da ƙarin nauyin biyan kuɗin haraji ba.
Ya jaddada cewa harajin da ake karɓa a halin yanzu ana amfani da shi ne wajen manyan ayyuka na ci gaba, kamar gina tituna da inganta muhalli a yankuna irin su Jiddari, da Umarari, da GRA,da Bulumkutu, da yankin Chad, da wasu muhimman wurare.
A cewar Farfesa Ibrahim Bello, jihar Borno ta samu ci gaba sosai wajen inganta tsarin haraji.

