Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da dakile wani taron badala da aka shirya gudanarwa a wani dakin taro a cikin birnin Kano mai taken “Bankwana da Shedan”.
A wani sakon murya da Mataimakin babban kwamandan Hisba a bangaren ayyuka na musamman da kai simame Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar ya aikewa da TST Hausa ya shaida cewa bayanan da hukumar ta samu ya nuna yadda wasu matasa maza da mata suna shirin sheke ayarsu har suke ikirarin cewa za suyi ban kwana ne da Shidan tunda ana daure shaidanu a watan Ramadan.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yanzu-yanzu-ganduje-ya-janye-shirin-samar-da-hisba-mai-zaman-kanta-a-kano/
Dr. Aminudden yace hakan yaci karo da koyarwar addinin musulunci kuma isgili ne ga addini.
TST Hausa ta rawaito cewa a yayin simamen domin dakile Yunkurin matasan an kama mutane tara (9) da ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da maza uku (3) da mata 6.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-haramta-samar-da-hisba-mai-zamanta-kanta-a-jihar/
Hukumar ta bayyana cewa an cafke wadanda ake zargin ne domin gudanar da cikakken bincike, tare da gano hakikanin manufar taron da kuma ko akwai wasu da ke da hannu a shirya shi.
Ta kara da cewa a halin yanzu ana ci gaba da bincike, kuma za a dauki matakin da ya dace bisa tanadin doka da zarar an kammala binciken.
Hukumar Hisbah ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ya saba wa doka, domin tabbatar da zaman lafiya da kyawawan dabi’u a jihar Kano.

