Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga daukacin al’umma da su bai wa lafiyarsu muhimmanci yayin gudanar da azumin watan Ramadan, tare da bin shawarwarin ƙwararrun likitoci domin kauce wa matsalolin da ka iya tasowa.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta fitar da sanarwar ta bakin kwamishinan ma’aikatar Dr. Abubakar Labaran Yusuf.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadan-gwamnan-sokoto-aliyu-ya-bada-umarnin-fara-biyan-maaikatan-jihar-albashin-fabareru-nan-take/
A wata sanarwa da mai magana da Yawun ma’aikatar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar yace ma’aikatar ta taya al’ummar musulmi murnar sake samun damar shaida watan Ramadan, tana mai jaddada cewa kula da lafiya na da matuƙar muhimmanci domin gudanar da ibada cikin ƙoshin lafiya.
Ma’aikatar ta shawarci masu fama da cututtuka na dindindin ko masu tsanani, ciki har da ciwon suga, da hawan jini,da gyambon ciki da cututtukan zuciya, da su tuntubi likitoci kafin fara azumi.
Hakan acewar sanarwar zai taimaka wajen daidaita shan magunguna da tsarin abinci cikin aminci.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadan-hukumar-hisbah-a-kano-ta-dakile-badala-mai-taken-bankwana-da-shedan-an-kama-matasa-9/
Haka kuma, an shawarci jama’a da su sha isasshen ruwa tsakanin buda baki da sahur, da kuma bukatar cin abinci mai gina jiki, su rage yawan fita a lokacin tsananin zafin rana, tare da hutawa yadda ya kamata. Ma’aikatar ta kuma bukaci jama’a da su gaggauta zuwa asibiti idan sun ji jiri, kasala mai tsanani ko wata alama da ba ta saba ba.
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da ci gaba da jajircewarta wajen kare lafiyar al’umma, tare da yi wa daukacin jama’ar jihar fatan Ramadan mai albarka cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

