Gwamnan Jihar Sokoto, Dakta Ahmad Aliyu, ya ba da umarnin fara biyan ma’aikatan jihar albashin watan Fabrairu na shekarar 2026 tun kafin ƙarshen watan, domin sauƙaƙa musu shirye-shiryen azumin watan Ramadan.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadangwamnatin-kano-ta-bada-umarnin-kara-lokacin-rufe-kasuwanni/
Sanarwar ta bayyana cewa za a fara biyan albashin daga ranar Juma’a 13 ga watan Fabrairu, 2026.
Matakin zai shafi ma’aikatan gwamnatin jiha, da ma’aikatan kananan hukumomi,da ma’aikatan ilimin firamare (LGEA), da kuma masu karɓar fansho.
Gwamnan ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ma’aikata damar tunkarar watan Ramadan cikin kwanciyar hankali da walwala, tare da samun damar biyan bukatunsu na yau da kullum.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadan-2026-gwamnatin-kano-ta-amince-dalibai-su-yi-azumi-a-gidajen-iyayensu/
Haka kuma, ya bukaci ma’aikatan da su ci gaba da nuna ƙwazo, da jajircewa da rikon amana a ayyukansu, yana mai jaddada kudirin gwamnatin sa na inganta harkokin mulki da kyautata jin daɗin ma’aikata a jihar.
Matakin ya samu karɓuwa daga ɓangarori daban-daban, inda ake ganin hakan zai taimaka wajen rage wa ma’aikata matsin tattalin arziki a wannan lokaci.

