Hukumar Gudanarwar Rahma Rediyo da Talabijin,Kano ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Mansoor Tallman Mai Faci Kwanar Jaba, ɗaya daga cikin masu biga waya a tashar, wanda ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
A yayin ziyarar, Alhaji Salisu Idris Yakasai, Shugaban Sashen Mulki na Tashoshin Rahma Rediyo da Talabijin, da ya wakilci Shugabar Hukumar Zartaswa, Hajiya Binta Sarki Mukhtar, ya bayyana alhinin da gidan ya yi saboda rasuwar marigayin.
KARIN LABARAI :https://tsthausa.com/mai-yawan-bada-gudun-mawa-a-gidaje-radiyo-a-kano-mansur-tallman-maifaci-kwanar-jaba-ya-rasu/
Ya ce rasuwar Mansoor babban rashi ne ga gidan Rahma,da abokan huldarsa masu buga waya yana mai jaddada cewa iyalansa da abokan aikinsa ba su kadai ba ne,sukayi rashi domin hukumar na tare da su a wannan lokaci mai wahala.
A yayin jawabinsa shugaban kungiyar kasu buga waya a kafafen yada labarai a kano, Kwamared Rabiu Akalata Dandago ya godewa hukumar zartaswa ta Rahma Rediyo da TV yana mai cewa Hajiya Binta Sarki Muktar ta ciri tuta saboda itace ta fara kai wannan ziyara a tsakanin masu gabatar da shirye shirye.
TST Hausa ta rawaito cewa Hajiya Binta Sarki Muktar ta bada babban buhun shinkafa da Taliya da kudi domin tallafawa iyalan Marigayin.
A ƙarshe, an yi addu’ar Allah Ya jiƙan Mansoor, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

