Shugaban Kasa Bola Ahamad Tinubu ya roki yan Najeriya da su koyi yadda ake rayuwa cikin sauki musamman Kashe duk wani kayan lantarki a cikin gidaje ko kasuwanni da basu da mahimmaci,wanda yace haka zai rage yawan kudin lantarki da ake biya.
Shugaba Tinubu ya bada wannan shawara ce a lokacin da yake mantawa da manema labarai a Lagos kai tsaye wanda shine karo na farko da yayi hakan.
A cewar Tinubu: Ba abu ne mara kyau ba idan ana cikin tsanani da tsadar rayuwa kuma ka koyi yadda ake rayuwa ciki sauki.
Bayan hawansa mulki, Tinubu ya kara kudin wutar lantarki bayan cire tallafin da gwamnati ke baiwa yan kasa.
A ranar 3 ga Afrilu na shekarar 2024, hukumar kula da hasken wutar lantarki ta Najeriya ta kara kudin lantarki ga Yan Najeriya da suke amfani da tsarin Band A, inda abokan ciniki ke biyan naira 225 a duk kilowatt guda daya kuma a kowanne awa, sabanin naira 66 da ake biya a baya.
Wannan mataki ya haifar da zazzafar suka ga gwamnatin Tinubu daga baya Kuma ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali.
Game da tashin farashin kayan abinci a kasuwanni da kuma bukatar gwamnati ta shiga dan a daidaita farashin ,Bola Tinubu yace bai yi imanin hakan ne ya janyo karuwar farashin kayan abinci a kasuwanni ba.
Saidai yace zaiyi duk mai yiyuwa dan wadata kasuwanni da kayan abinci.

