Mahaifin maigidan Maryam Sanda, Alhaji Ahmad Bello Isa, ya bayyana cewa ya yafewa Maryam Sanda wadda aka daure bisa laifin kashe mijinta, marigayi Bilyaminu Bello, tare da goyon bayan afuwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bata kwanan nan.
Alhaji Ahmad Bello ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce yafe wa Maryam Sanda shi ne matakin da ya dace domin samun zaman lafiya, domin kuwa ramawa ba za ta dawo da ɗansa ba. Ya ce tun kafin hukuncin kotu, ya riga ya rubuta wasiku zuwa ga Ma’aikatar Shari’a da Hukumar ‘Yan sanda yana roƙon a yi mata afuwa saboda yaran da ta bari.
TST Hausa ta rawaito a watan Janairu na shekara ta 2020 ne Babbar Kotun Abuja ta same ta da laifin kisa, inda ta yanke mata hukuncin kisa. Sai dai a watan Oktoba 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya sunanta cikin jerin mutane 175 da aka yi wa afuwa ta musamman.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan uwansa marigayin sun bayyana rashin jin daɗinsu game da wannan afuwa, suna mai cewa wannan mataki ya sake buɗe musu raunin da suke ƙoƙarin mantawa da shi, tare da bayyana cewa hakan babban zalunci ne ga adalci.
Wannan lamari dai ya haifar da muhawara tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin afuwar ta nuna tausayawa da jinƙai, yayin da wasu ke ganin hakan na iya raunana amincewar al’umma ga tsarin shari’a a ƙasar.

