Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta nuna damuwa akan yadda yawancin yan Najeriya suka ki biyayya ga umarninta na kashe wayoyin hannu daga karfe 11 na safe zuwa karfe 2 na rana saboda karin kuɗin kiran waya da Data da kaso 50 cikin 100 da Kamfanonin sadarwa sukayi.
A ranar 13 ga watan Fabarerun shekarar 2025 ne Kungiyar ta NLC ta nemi yan Najeriya su rika kashe wayoyinsu nasu har zuwa ranar 1 ga watan Maris.
Saidai a yayinda yake aikewa da sakon murya ga Jaridar TST Hausa, daya daga cikin dattawan Kungiyar Kwadago a Arewancin Najeriya sannan tsohon Shugaban Kungiyar a Kano Kwamared Ali Mannir Matawalle ya nuna bacin ransa saboda bayan bijirewa umarnin Kungiyar harda masu zaginsu akan umarnin da suka bayar.
Kwamared Matawalle yace, yawancin ma’aikatan Najeriya ne kadai suke kashe wayoyin daga ranar laraba da aka bada umarnin kuma suma sunfi yawa daga Kudancin Najeriya.
Ya kara dacewa amma,yan Najeriya basu bi umarnin ba ,a dan haka suna sane da hakan,harda zage zagen da akayi musu a shafukan sada zumunta na zamani.
“Muna tsoron ranar da za’a wayi gari mu daina kare hakkin yan Najeriya,mu daina kwato musu yancinsu,mu koma kare bukatun ma’aikata da yan fansho kadai a Najeriya”,Inji Matawalle
Ya kuma nuna gamsuwarsa abisa yadda kamfanin sadarwa na MTN ya baiwa yan kasa hakuri akan wani kari da yayi na kaso 200 cikin 100 na kiran waya da saka Data,duk dacewa neman afuwar ba akan karin da suke ja inja akai ba ne tsakaninsu da Kamfanonin sadarwar.
A karshe ,Ali Mannir Matawalle ya nemi yan Najeriya da su fito su fadawa NLC laifin da sukayi musu idan har akwai ,saboda yawan bujirewa kiranta da yan kasa suke yi a duk lokacin da bukatar kiran ya taso.

