Tsohon Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina, ya bayyana cewa kafa hukumar Hisbah Gandujiyya ba wani yunkuri ba ne na fito-na-fito da gwamnatin jihar, kamar yadda wasu ke hasashe.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/an-kaddamar-da-takardar-daukar-yan-hisba-masu-zaman-kansu-na-gandujiyya-a-kano-2/
Sheikh Ibn Sina ya ce Hisba Gandujiyya an kirkire ta ne domin ci gaba da tallafawa al’umma da gudanar da ayyukan addini da na alheri ba tare da sabawa doka ko gwamnati ba.
Ya shaidawa TST Hausa cewa samar da hukumar zai bada gudunmawa kari akan abinda gwamnati keyi a jihar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-zai-kafa-sabuwar-hukumar-hisba-mai-zaman-kanta-a-kano/
Ya kuma kara da cewa nan ba da jimawa ba za su kai ziyara gaisuwa ga Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin neman albarka da kuma bayyana cikakken manufar kafa Hisbah Gandujiyya.
Sheikh Ibn Sina ya tabbatar da cewa burinsu shi ne su yi aiki tare da hukumomi wajen wanzar da tarbiyya, tsaro da kyawawan dabi’u a cikin al’umma.

