Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero,yace babu wani gwamna da ke da hurumin haramta ayyukan kungiyar kwadago a jihar da yake mulki duk da kasance shine gwamna mai cikakken iko.
Ajaero ya kuma shaida cewa karfin ikon kungiyar NLC yana karkashin jerin ‘dokokin da yan majalisar tarayyar suka samar cikin kundin tsarin mulkin kasa.
Yana wannan kuka ne a lokacin da yace yawancin gwamnonin Najeriya sun koma Abuja da zama din din din sun bar al’umarsu cikin kuncin rayuwa.
Ajaero yana kuma mayar da martani ne game da haramta kafa kungiyoyin kwadago a jami’oin jihar Kogi da tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello, ya yi a zamanin mulkinsa.
Shugaban NLC din na Najeriya na kokarin dawo da wannan zance ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya halarta da garin Lakoja a jihar ta Kogi
Tun da farko ma’aikatan jihar Kogi sun shaida wa Shugaban NLC cewa sama da shekaru 10 kenan kungiyoyin kwadagon da ke Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi, da Jami’ar Jihar Kogi, da Kwalejojin Ilimi, da na Fasaha, da Ma’aikatan Jinya suke cikin wani hali bayan da gwamnatin jihar ta nuna adawa da samar da kungiyoyin ma’aikata a inda suke aiki.
“Ina nanata cewa babu wani gwamna a Najeriya da yake da ikon hana aiwatar da ayyukan yan Kwadago a ko ina a Najeriya,kuma na sake fada cewa babu wani mutum da yake da ikon hana abinda bashida da iko a kansa.
Shugaban NLC, wanda ya bayyana mamakinsa da cewa akwai irin wannan abu da yake faruwa a matakin jiha na kokarin hana ma’aikata su kafa kungiyoyin a maikatun dake karkashin Jihar wanda yace haramun ne yin hakan a dokar kasa.
Shugaban Kungiyar na NLC yace sun gano yawancinsu irin wadannan gwamnonin sune suke barin jihohinsu su koma Abuja da zama gaba daya, yayin da al’ummarsu da ya kamata su mulka suka barsu cikin halin kaka nakayi.
Saidai yace akwai fata na barin ma’aikata suyi aikinsu cikin yanayi mai kyau a yanzu tunda gwamna maici na yanzu da mataimakinsa duka tsaffin Shugabanni ne a Kungiyar Kwadago ne .

