Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya cewar an dawo da jami’ar Northwest sunanta na asali ne domin taci gaba da rike kanbunta da kuma darajarta .
Gwamnan Yusuf ya bayyana hakan yayi zaman majalisar zartaswa wanda ya jagoranta a fadar gwamnatin jiha.
Ya kara da cewar a yanzu kuma an mayar da sunan Kwalejin ilimi ta karamar hukumar Ghari, zuwa Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced studies.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2017 ne tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sauya sunan jami’ar ta Northwest university zuwa Yusuf Maitama Sule domin karrama marigayi dan masanin Kano Dr Yusuf Maitama.
A ranar 19 ga watan Satumba na shekarar 2024 gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Shima ya dawo da sunan Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi asalin sunanta na Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi.

