Majalisar Masarautar Kano ta karɓi bakuncin shugabannnin rajin samar da Zaman Lafiya na Arewa 2026, ƙarƙashin jagorancin Jakadan Zaman Lafiya na Duniya, Ambasada Zubairu Dalhatu Malami, domin tattaunawa mai zurfi kan ƙarfafa haɗin gwiwa wajen samar da zaman lafiya da juriya a cikin al’umma a Arewa maso Najeriya.
Taron, wanda aka gudanar a gidan Magajin Garin Kano, Alhaji Muhammad Nasiru Wada, ya mayar da hankali ne kan gabatar wa Majalisar Masarautar manufofi da tsare-tsaren kamfen ɗin, tare da duba hanyoyin haɗin gwiwa da hukumomin gargajiya wajen magance matsalolin tsaro, raunin matasa, da ƙaruwa rikice-rikicen zamantakewa a yankin.
A yayin ziyarar, tawagar samar da zaman lafiya da manyan ginshiƙan shirin, waɗanda suka haɗa da wayar da kan jama’a,da motsa al’umma, ƙarfafa matasa da mata, da kuma amfani da tsarin Gargaɗin Farko da Daukar Mataki Cikin Gaggawa watoEarly Warning and Early Response) ta hanyar fasaha, tare da haɗin gwiwa da Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya da Rikici.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hukumar-sharia-ta-kano-ta-kammala-taron-bita-ga-limaman-kano-na-kwana-biyu/
Da yake jawabi a madadin Mai Martaba Sarkin Kano, Magajin Garin Kano ya yaba da wannan yunƙuri, tare da jaddada muhimmiyar rawar da hukumomin gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya nuna buƙatar aiwatar da shirye-shiryen da ke magance tushen matsalolin tsaro, ciki har da ƙaura daga karkara zuwa birane, rashin aikin yi, da ƙarancin damammaki ga matasa.
Ya kuma shawarci shugabannin samar da.kamfen ɗin da su kiyaye tsaka-tsaki yayin da ake tunkarar zaɓen siyasa na 2027, tare da neman a gabatar da bayyanannen jadawalin irin gudunmawar da ake buƙata daga Majalisar Masarautar Kano.
Majalisar Masarautar Kano ta bayyana shirinta na bayar da cikakken goyon baya ga ayyukan kamfen ɗin a matakin ƙananan hukumomi, tare da haɗin gwiwa wajen ƙarfafa tsarin gargaɗin farko da daukar mataki cikin gaggawa a cikin al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kano-ta-fara-gasa-da-biranen-afurika-a-fannin-kasuwanci-da-zuba-jari-in-ji-gwamna-yusuf/
A nasa jawabin, Ambasada Zubairu Dalhatu Malami ya nuna godiya matuƙa ga Majalisar Masarautar Kano bisa kyakkyawar tarba, tare da jaddada aniyar kamfen ɗin na yin aiki kafada da kafada da hukumomin gargajiya, hukumomin gwamnati, da abokan hulɗar ci gaba domin bunƙasa zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kan al’umma a Arewa maso Najeriya.
Ziyarar ta ƙare da zagayawa a Cibiyar ICT ta Muhammad Inuwa Wada, wadda Magajin Garin Kano ya kafa, sannan aka ɗauki hoton haɗin gwiwa.
Kamfen Din Zaman Lafiya na Arewa 2026 shiri ne na haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da dama, wanda ake aiwatarwa tare da haɗin gwiwar Africa Peace Reform Initiative Zamkah Technologies Limited, IPCR, AUDA-NEPAD Najeriya, Global Peace Chain, da Coral Charitable Foundation.

