Daya daga cikin masu yawan sauraren gidajen Radio a Kano Mansur Tallman Maifaci, Kwanar Jaba, ya rasu bayan fama da matsananciyar rashin lafiya, lamarin da ya girgiza al’ummar Jaba da ma masu sauraron shirye-shiryen rediyo a fadin jihar Kano da kewaye.
Marigayin wanda matashi ne dake dogaro da kansa ya shafe shekaru yana bada gudun mows a shirye-shiryen rediyo daban-daban, inda ya yi fice wajen bayar da sharhi da tattaunawa kan al’amuran zamantakewa,da gargajiya da kuma ci gaban al’umma.
Sannan yana bada gudun mowa wajen tura sakonnin musamman shirin Karkade kunnuwa na Rahma Radiyo Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa Saboda irin salon maganarsa mai jan hankali da fahimtar jama’a, shirye-shiryen da yake halarta sun samu yawan sauraro, musamman a lokutan da ake tattauna batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum.
Masu sauraro da dama sun shaida cewa muryarsa da hangen nesansa sun taimaka wajen wayar da kan al’umma, tare da karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya dade yana jinya kafin rasuwarsa. Har zuwa lokacin hada wannan labari, ba a sanar da cikakken lokaci da wurin jana’izarsa ba, sai dai an ce za a bayyana hakan nan gaba, in sha Allahu.
Mansur Tallman Maifaci ya rasu ya bar baya da iyali, ‘yan uwa da kuma dimbin masoya, musamman daga cikin masu sauraron rediyo da abokan aikin sa.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya kyautata makwancinsa, Ya kuma jikan dukkan al’ummar da ya bari a baya. Amin.

