Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarni ga jami’an ’yan sanda da ke gadin manyan mutane (VIPs) su koma ayyukansu na asali na kula da tsaro a cikin al’umma, yayin da ya bada umarnin ga rundunar tsaro ta civil defense NSCDC ta karɓi nauyin tsaron VIP daga yanzu.
Wannan umarni ya fito ne bayan kammala taron gaggawa kan tsaro da aka gudanar a fadar gwamnati dake Abuja, wanda ya samu halartar manyan hafsoshin tsaro, ciki har da Shugaban Rundunar Soja,da Shugaban Rundunar Sama, da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, da Daraktan DSS.
Karin Labarai:https://tsthausa.com/6407-2/
A cewar sanarwar mai magana da yawun Shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, matakin ya zama dole saboda karancin jami’an ’yan sanda a sassan ƙasar nan, lamarin da ke rage ingancin aikin tsaro a yankunan karkara da birane.
Tinubu ya kuma amince da daukar sabbin ’yan sanda 30,000, tare da aiki da jihohi domin inganta cibiyoyin horaswa domin kara karfin rundunar.
Karin Labarai:https://tsthausa.com/6390-2/
Da wannan sabon tsari, duk wani babban mutum da ke bukatar jami’an tsaro zai nemi su ne daga rundunar tsaro ta Civil Defence maimakon rundunar ’yan sanda.
Masu sharhi na ganin wannan mataki zai kara yawan jami’an ’yan sanda a kan tituna, amma kuma yana bukatar karfafa rundunar ta NSCDC domin su iya daukar nauyin tsaron manyan mutanen cikin ƙwarewa.

