Kungiyar yan jarida masu Wallafa labarai a yanar Gizo wato Kano Online Media Chapel ta taya murnar samun lambobin yabo da aka bai wa kwamishinan yada labarai na Kano Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya,Sunusi Bature Dawakin Tofa Daraktan Yada Labarai ga Gwamnan Jihar Kano da tsohon kwamishinan yada Labarai na Kano Baba Halilu Dan Tiye a taron mika lambobin yabo da kungiyar yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano ta gudanar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/waiya-da-shugaban-nuj-na-najeriya-sun-bu%c9%97e-ofishin-yan-jarida-na-online-a-kano/
A cikin sanarwar da Shugaban Kano Online Media Chapel, Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya fitar, ya bayyana cewa an bai wa wadannan fitattun shugabanni lambobin yabo ne saboda gudummawar da suka bayar wajen bunkasa harkar yada labarai, da kuma kare martabar aikin jarida a jihar Kano.
Dangambo ya yi karin haske kan irin rawar da Hon. Waiya ke takawa wajen bude hanyoyin hulda da manema labarai da tabbatar da sahihancin bayanai ga jama’a.
Haka kuma, ya yaba wa Sunusi Bature bisa jajircewarsa wajen tsara da daidaita harkokin sadarwa a gwamnatin Jihar Kano, da kuma Baba Halilu Dan Tiye saboda gudummawarsa wajen bunkasa aikin jarida da horas da sabbin ma’aikata a masana’antar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/majalisar-wakilai-na-maraba-da-duk-wata-doka-zata-inganta-walwalar-yan-jarida-a-najeriya-abbas/
Kungiyar ta bayyana cewa irin wannan yabo na kara karfafa gwiwa ga shugabanni da masu rike da mukamai domin ci gaba da tallafawa aikin jarida na gaskiya da nagarta.
A karshe, Kano Online Media Chapel ta yi fatan cewa reshen NUJ na Jihar Kano zai ci gaba da gudanar da shirye-shiryen karrama kwararru a harkar jarida domin karfafa aiki mai nagarta a jihar.

