Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ce ya fara tunanin yiwuwar sayar da matatun man ƙasar nan.
Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ne, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Bloomberg.
Ya ce yanzu haka kamfanin yana sake duba yadda ake gudanar da matatun, kuma ana sa ran kammala wannan nazari kafin ƙarshen shekara.
Jarida Daily Truth ta rawaito cewa da yake magana a taron Kungiyar kasashen duniya masu arzikin man fetur OPEC karo na tara da aka yi a Birnin Vienna, na ƙasar Austria, Ojulari ya ce gyaran tsofaffin matatun gwamnati ya wuce yadda ake tsammani.
Najeriya na da matatu huɗu; Fatakwal, Warri da Kaduna, amma sun daɗe suna fama da matsaloli kuma ba sa aiki yadda ya kamata.
A watan Nuwamban 2024, NNPCL ta sanar da cewa matatar Fatakwal ta fara tace mai, amma daga bisani aka rufe ta a watan Mayun 2025 saboda matsalolin da suka shafi gyara.
An daɗe ana kiranye-kiranyen bayar da su ga kamfanonin masu zaman kansu domin kula da su yadda ya kamata.

