Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta wanke tare da sallamar ɗan gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Muhammad Mahadi Shehu, da kamfaninsa Dialogue Global Links Limited, daga dukkan tuhume-tuhume guda shida da Ofishin Babban Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya shigar a kansu, a madadin tsohuwar Gwamnatin Jihar Katsina.
An shigar da karar ne tun a shekarar 2021, inda ake zargin Mahadi Shehu da aikata laifukan bata suna ta kafafen sada zumunta, yaɗa takardun bogi, da kuma watsa bayanan ƙarya da ake cewa sun haifar da damuwa ga jami’an Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Tsohon gwamna Aminu Bello Masari.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yaudara-ta-akayi-nayi-belin-dilan-kwaya-a-kotuina-neman-afuwar-jamaa-kwamishina-namadi/
Yayin karanta hukuncin mai shafuka 70, wanda ya ɗauki kusan sa’o’i biyu, alkalin shari’ar, Mai shari’a Simon Amobeda, ya bayyana cewa masu gabatar da ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da suka dace domin tabbatar da tuhume-tuhumen da suka shigar.
Kotun ta ce shaidun da aka gabatar ba su da ƙarfi kuma ba su gamsar ba, inda ta yanke hukuncin cewa ba a tabbatar da ko ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen guda shida ba tare da shakku ba, kamar yadda doka ta tanada.
Masu gabatar da ƙarar sun kira shaidu guda shida daga Ofishin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da kuma Gwamnatin Jihar Katsina.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/babbar-kotun-jiha-tayi-barazanar-sanya-kafar-wando-daya-da-duk-wanda-ya-sake-tozarta-sharia-a-kano/
Shugaban tawagar lauyoyin Mahadi Shehu, Barrista Mustapha Abubakar, SAN, ya yabawa kotu bisa abin da ya kira hukunci mai zurfin tunani da adalci, wanda ya nuna ’yancin kai da bin doka a bangaren shari’a.
Da yake zantawa da ’yan jarida bayan kammala shari’ar, Mahadi Shehu ya ce shari’ar ta ɗauki kusan shekaru huɗu, ta hannun alkalai huɗu, inda ya jaddada cewa hakan ba zai hana shi ci gaba da gwagwarmayarsa ba.
A ɓangaren masu gabatar da ƙarar, Barrista Badamasi Garba ya ce za su duba cikakken kwafin hukuncin kotun kafin yanke shawara kan mataki na gaba.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da aka dade ana yi wa Mahadi Shehu da kamfaninsa, wadda ta ja hankalin al’umma a faɗin ƙasar nan tun daga shekarar 2021

