Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya jajantawa al’ummar Kano kan abinda ya faru na kasan gilla da aka yiwa Hausawan Arewa a yankin Uromi dake jihar Edo wadanda yawancinsu yan Kano ne.
Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a yayinda ya kawo ziyara ta musamman jihar Kano ranar litinin.
“Mahaifina ya zauna a Hotoro da Gyadi Gyadi ,kuma Ina yawan zuwa Kano tun Ina matashi,a dan haka ba zan bari a cutar da Kano da mutananta ba”Inji gwamna Okpebholo.
Yace sunzo Kano shida tawagarsa domin mika sakon ta’aziya kan kisan gillar da akayiwa yan asalin kano a Edo da kuma tabbatar da cewa za’ayi adalci.
Gwamnan yace a yanzu haka an kama mutane 14 da ake zargin suna da hannu wajen kashe hausawan yan asalin Kano kuma suna tsare a yanzu haka.
Gwamnan na Edo yace ba dan ana hutun sallah karama ba ,da tuni an mika mutanan Abuja kamar yadda babban sifeton yan sandan Najeriya ya bada umarnin hakan.
Ya tabbatarwa mutanan Kano cewa , za’ayi adalci a wannan Lamari da ya faru a Edo.
Anasa jawabin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna takaicinsa kan abinda ya faru a jihar ta Edo ga al’ummar hausawan na Kano,yana mai cewa zasu hada kai da gwamnan na Edo domin tabbatar da adalci.
Haka kuma gwamna Yusuf ya godewa gwamnan na Edo Monday Okpebholo abisa yadda ya nuna damuwa da kuma matakan da ya dauka na tabbatar da adalci ciki harda dakatar da ayyukan yan sintiri da aka samar ba bisa ka’ida ba a jihar.
Gwamnan na Kano yace , a madadin kanawan dabo,yana bukatar a nunawa duniya mutanan da aka kama domin kowa ya gansu, sannan a kaisu kotu,yana mai kira ga gwamnan na Edo da ya jagoranci biyan diya ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Gwamna Yusuf ya kuma ce zai jagoranci raka gwamnan zuwa kananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya domin jajantawa iyalan mafarautan da aka kashe a jiharsa.
Daga nan gwamna Yusuf ya sake rokon jama’ar Kano musamman matasa da su guji daukar doka a hannunsu.
Ya kuma ce a yanzu mutanan Kano sun zura ido suga irin adalcin da za’ayi kan kisan gillar da akayiwa Hausawan na Arewa a Edo.

