A yayinda ake cigaba da taron sanin makamar aiki da gwamnatin Kano ta shiryawa yan jarida masu rubuta labari a kafafen sadarwa wato Online newspaper dake gudana a garin Dutse jihar Jigawa Farfesa Nura Ibrahim daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) ya ja kunnen ‘yan jarida masu aiki a kafafen intanet kan muhimmancin yin rahoto cikin gaskiya, ladabi, da mutunta jama’a.
Farfesan ya bayyana cewa ‘yan jarida su guji amfani da kalmomi masu tada hankali ko jefa jama’a cikin rikici.
Ya kara da cewa dole ne a tabbatar da gaskiyar labarai kafin a wallafa su, sannan a gyara kuskure cikin hanzari idan an samu.
Haka kuma, Farfesan ya yi kira ga ‘yan jarida da su kauce wa yada labaran karya da jita-jita, su kuma dogara da sahihan tushe da bincike mai inganci.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/waiya-da-shugaban-nuj-na-najeriya-sun-bu%c9%97e-ofishin-yan-jarida-na-online-a-kano/
Ya bayyana cewa bin ka’idojin aikin jarida na zamani yana kara amincewar jama’a, sannan yana tabbatar da cewa rahotanni a intanet suna zama masu gaskiya, tsafta, da jan hankali ga masu karatu.
Taron, wanda Gwamnatin Jihar Kano ta dauki nauyi ta Ma’aikatar Labarai da Harkokin cikin gida, an shirya shi ne domin karfafa ilimi da kwarewa ga ‘yan jarida, musamman wajen yadda za su gudanar da aikin jarida na zamani cikin gaskiya da adalci.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kungiyar-yan-jarida-na-kano-online-ta-taya-waiya-sunusi-bature-da-dan-tiye-murnar-kyautar-da-nuj-ta-basu/
TST Hausa ta rawaito cewa tun a ranar bude taron Kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya da shugaban kungiyar yan jairda na kano online chapel Kwamared Abubakar Dan Gambo sun nemi mahalarta taron da su rika aiki cikin gaskiya.

