Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah Wadarai da kalaman tsohon gwamnan jihar Dr.Abdullahi Umar Ganduje da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibiril akan tsaron Kano wanda hakan ya janyo aka kawo hare hare wasu kananan hukumomin jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya shaida hakan a taron manema labarai kan abinda zaman majalisar zartaswar jihar ya kunsa karo na 34.
Majalisar Zartaswar ta amince da Kashe kuɗade sama da naira Biliyan 54 domin aiwatar da ayyukan raya kasa a jihar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-zai-kafa-sabuwar-hukumar-hisba-mai-zaman-kanta-a-kano/
Kwamishinan Wayya yace zaman majalisar zartaswar ya amince da bukatar kama Ganduje da Barau domin tuhumarsu kan zargin hana Kano zama lafiya.
TST Hausa ta rawaito cewa,a kwanan nan ne Dr Ganduje yayi ikararin kafa sabuwar hukumar Hisba mai zaman kanta ta Jihar karkashin kulawarsa abinda gwamnatin Kano tace ya saba doka Kuma takalar rigima ne da tada fitina.
Bayan ikirarin kafa Hisba mai zaman kanta, Gwamnatin Kano ta kuma zargi Ganduje da wasu kalaman tunzuri akan sha’anin tsaro wanda ya sabawa Doka.
Haka Kuma gwannatin ta zargi Sanata Barau Jibiril da tunzura jama’ar Kano saboda kalaman da yayi na cewa Kano ta koma baya abinda shima ya janyo Cece-Kuce.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/da-a-haifi-yara-marasa-tarbiyya-a-auren-zaurawa-a-kanokara-a-samar-da-ruwan-sha-in-ji-tsohon-hadimin-ganduje/
Gwamnatin ta nemi hukumomin tsaro da su tabbatar sun kama Ganduje da Barau domin tuhumarsu.
Gwamnatin Kano ta kuma shawarci jama’a da su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin yadawa, domin kaucewa tayar da hankulan jama’a bisa labaran da ba su da tushe.

