Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya nuna matuƙar alhini kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a Kano.
Rt. Hon. Rurum ya bayyana marigayin a matsayin ginshiƙi a harkokin kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki, inda ya ce gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a Kano da Najeriya baki ɗaya.
Haka kuma, Rt. Hon. Rurum ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano da kuma iyalan Fatima Abubakar, wadda aka kashe tare da ’ya’yanta guda shida a Dorayi Chiranchi, Karamar Hukumar Kumbotso.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/matashin-da-ya-jagoranci-taaddancin-dorayi-shine-ake-zargi-da-kone-mata-biyu-a-tudun-yola-in-ji-yan-sanda/
Dan majalisar ya yi Allah-wadai da wannan mummunan aiki, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta bincike tare da tabbatar da cewa duk masu hannu a laifin sun fuskanci hukunci bisa doka.
Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya jiƙan mamatan da rahama, Ya kuma ba iyalan da suka rasa nasu ƙarfin jure wannan babban rashi.

