Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya halarci sallar Juma’a a wani masallaci da ke birnin Legas, inda Limamin masallacin ya shawarce shi da ya kasance mai haƙuri da tsayin daka wajen tafiyar da al’amuran shugabanci.
A cikin hudubar Juma’ar, Limamin masallacin juma,ar na Lekki Dr. Salahudeen Arriyadhi ya bayyana cewa babu wani shugaba da zai iya gamsar da kowa, yana mai jaddada cewa shugabanci na tattare da yanke shawara mai wahala da kuma fuskantar suka daga al’umma.
Dr. Salahudeen ya bukaci Shugaba Tinubu da kada ya bari irin wadannan kalubale su raunana masa gwiwa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-zai-shiga-shekarar-2026-da-farawa-da-ciwo-bashin-tiriliyan-17/
Limamin ya kuma ja hankalin shugaban ƙasar da ya ci gaba da ɗaukar matakan da yake ganin sun dace domin cigaban ƙasa, tare da la’akari da adalci da jin ƙai ga talakawa.
Haka kuma, an gudanar da addu’o’i na musamman domin Allah Ya ba Shugaban ƙasar hikima, ƙarfi da shiriya wajen jagorantar Najeriya, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Shugaba Tinubu ya halarci sallar tare da wasu manyan jami’an gwamnati da kuma dimbin al’ummar Musulmi, lamarin da ya ja hankalin jama’a da dama.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/muna-bukatar-tinubu-ya-yiwa-yan-kasa-bayani-na-gamsarwa-kan-harin-amurika-a-najeriya-sakon-pdp-ga-tinubu/
Masu ibada sun bayyana fatan cewa shugabannin ƙasa za su yi anfani da irin wadannan shawarwari na addini wajen tafiyar da harkokin mulki domin samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
TST Hausa ta rawaito cewa daga cikin wadanda suka raka Shugaba Tinubu halartar sallar Juma’a sun hada da mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu da mataimakin gwamnan Jihar Legas, Dr. Obafemi Hamzat da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila da sauransu.

