Hukumar gudanarwa ta jami’ar Sharda dake kasar Indiya ta karrama gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne abisa jajircewarsa wajen cigaban Ilimi a Kano.
Jami’ar tace irin gudun mowar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya baiwa jami’ar ta Sharda tun zamanin sanata Rabiu Musa kwankwaso a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 yasa ta karrama gwamnan Kano.
A kalla dalibai 1,001 gwamna Abba ya dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen Indiya da Uganda domin karo karatun digiri na biyu.
A watan Oktoban 2024 gwamna Yusuf ya tura daliban karo karatu
Rahotanni nacewa gwamnan yaje Indiya ne duba daliban,daga nan jami’ar ta Sharda ta karrama shi.

