Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta kammala wani taron horaswa na tsawon kwana uku da ta shirya wa limamai daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, domin kara inganta iliminsu kan harkokin addini, zaman lafiya da warware matsalolin al’umma.
Taron horaswar, wanda ya samu halartar daruruwan limamai, ya mayar da hankali kan rawar jagoranci da limamai ke takawa wajen tabbatar da adalci, dakile rikice-rikice, da wayar da kan jama’a game da muhimmancin zaman lafiya da bin doka.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kalaman-ganduje-na-kafa-hisba-da-na-barau-akan-cigaban-kano-su-ne-suka-janyo-rashin-tsaro-a-jihar-gwamnatin-kano/
Yayin rufe taron, Kwamishinan Harkokin Addinai, Sheikh Tijjani Auwal, ya jaddada matsayin limamai a matsayin tubalan gina zaman lafiya da tarbiyya a cikin al’umma. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafawa irin wadannan shirye-shirye domin dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Shi ma a nasa jawabin, Kwamishina na Biyu, Sheikh Ali Danabba, ya gode wa limaman bisa halartar taron tare da bayyana cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen gyaran halayen matasa da sasanta rigingimun cikin gida. Ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta kara zurfafa hadin kai da limamai don ci gaba da shirya karin horaswa a matakai daban-daban.
Hukumar Shari’a ta bayyana cewa wannan horaswa na daga cikin muhimman dabarun gwamnatin Kano na karfafa gwiwar shugabannin addini domin su ci gaba da ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

