Daga Adamu Muhammad Nababa.
GUGUWA A CIKIN KAFO SHAYI !!!
Lallai ranar Lahadi 15 /12/2024 rana ce mai tarihi da haske a bangaren Ilimi a Kano gata Kuma tazo ƙarshen mako wacce ta dace da ranar karshen ta hutun da su kansu dalibai keyi.
A bangarena nima na himmatu da hutun karshen mako Ina karanta jaridu kawai Sai idona ya tsinci kanun jaridar Daily Nigerian da Jaafar Jaafar ya wallafa na cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sauyawa wasu shugabanni wuraren aikinsu hakan yasa na gyara zama sosai.
Ba a gama mantawa da abinda ya faru ba na ranar Alhamis wato sauye-sauyen da aka samu a Majalisar zartaswa ta gwamna inda Gwamna ya ba wa irin su Sagagi da Bichi takalma su saka su kara gaba.
Sai kwatsam Kuma wani abokin aikina ya kira ni ya ce an samu canji a wasu hukumomin jihar da Gwamna ya sakeyi.
Sai ya aiko min da Sanarwa na Jaridu suka wallafa cewa an dauke Kabiru Ado Zakirai, daga hukumar kula da makarantun sakandire ta kano wato KSSSMB zuwa dakin karatu na gwamnatin jiha.
Kafin na tambayeshi wa aka kawo kuma,sai ya turon sunan Hon Rabiu Sale Gwarzo da zai maye gurbinsa.
Samun labarin hakan sai naji kamar wani juyin mulki akayi a kasar da ake mulkin kama karya.
A zahirin gaskiya bamuyi mamaki ba Kuma dama mun dade Muna cewa kamar wanda ya tafi, bai shirya ba,ya karbi matsayin da aka bashi Wasu ma na zargin bai dace ba kuma bai cancanta ba.
Bugu da kari dan kadan ya sani game da Hukumar, haka abubuwa sukaita tafiya har saida shi kansa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fahimci matsalar da kansa.
Wannan hukuma ta KSSSMB ba hukuma bace da za’ayi wasa da ita ba .
JAGORANCIN JAGORA
Ina da sha’awa ta musamman kan wannan rubutu domin kuwa Zakirai ya kasa baiwa KSSSMB shugabancin da ake bukata domin hukumar ta cimma muradun ilimi da aka sa gaba.
Duk yadda ake bashi shawarwari yaki dauka saboda ma daukar kansa yake kamar Wanda ya kware a bangaren ilimi ,to Amma abinda muka sani shine komai nisan gona akwai kunyar karshe Kuma yau anga kunyar karshe
WACCE RAWA SHUGABANNNI HUKUMAR KSSSMB SUKA TAKA A BAYA?
Hukumar KSSSMB ta doru akan saiti bayan da ta hadu da mai jini a jika dan shekara 41 mai karatun digiri na uku (PhD) Wanda Kuma ba kowa bane illa Dr Bello Shehu wanda kuma yasan makamar aiki yayi duk mai yiyuwa wajen daga darajar hukumar ta KSSSMB.
Kafin zuwan Dr Bello Shehu, hukumar ta kuma samu Shugaba irinsa mai digirin digirgir Wato Dr Husaini Abdullahi Ganduje,Kuma Shima anga irin rawar da ya taka wajen daga darajar hukumar.
Hukumar ta KSSSMB ba kuma zata manta da gudun mowar da Hon Habib Hassan El-Yakub ya taka wajen ciyar da Hukumar gaba kasancewarsa Shima goga ne yasan hanya irinsu Dr Bello Shehu.
SAUYI BA TSAMMANI
A wannan lokaci bayan hukumar ta KSSSMB ta dauki tsawon shekara daya da watanni tana cikin wani hali,a gefe daya kuma ana ta yiwa gwamna rufa rufa a bangaren Ilimi,sai kwatsam ya gwamna ya gaggauta ceto bangaren Ilimi baki dayansa daga neman lalacewar da ya dauko aka sauya Shugaban hukumar ta KSSSMB bayan shi kansa kwamishinan ilimi na Kano da aka sauya .
To me ya ragewa hukumar a yanzu shine sai a sake zuba Ido dan ganin abinda Sabon shugabanta Hon Rabiu Sale Gwarzo yazo dashi .
Wasu na ganin da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bai gaggauta ceto ilimin kano daga neman durkushewa ba to fah da duk burin gwamnan na fifita ilimi zai kare ne wajen fifita kashin Kai daga wasu da ake ganin shafaffu da mai ne musamman yadda ya ware kaso 31 cikin dari a kasafin kudin shekarar 2025 da sai shekarar ta kare Babu abin Azo a gani.
Tunasarwa ga duk Wanda zai rike hukumar KSSSMB da sauran hukumomin ilimi su gane cewa ilimi rai ne dashi kana shakeshi sai jiki ya gane .
Na gode

