Babban Limamin masallacin Juma’a na Alfurqan dake Unguwar Nasarawa GRA Dr. Bashir Aliyu Umar ya yi kira ga musulmi da su kula da tsabtace jikinsu,da tufafinsu da jikunan su kafin su halarci Sallar Juma’a.
Ya ce ana samun mutane da ke zuwa masallaci cikin wari,da datti ko gumi, al’amarin da ya bayyana a matsayin cin fuskar masallata da kuma cutar da Mala’iku masu halartar sallar.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/hudubaabinda-yafi-komai-dadi-a-aljanna-shine-ganin-allahmasu-ciyarwa-sune-a-gaba-dr-nasir/
Dr. Bashir ya bayyana cewa masallaci wurin ibada ne, kuma Musulunci ya yi tsauraran dokoki kan tsafta da kammala shiri kafin sallah.
Ya ce mazaunin masallaci ba wurin wari ba ne, don haka musulmi ya kamata ya tabbatar da ya yi wanka,da amfani da turare, sannan ya wanke bakinsa kafin ya yi niyyar zuwa sallar jam’i ko Juma’a.
Malamin ya yi nuni da cewa Annabi (SAW) ya haramta kusantar masallaci ga wanda ke da wari mai cutarwa, musamman wari irin na tafarnuwa,da albasa ko duk wani wari da zai takura wa jama’a da Mala’iku.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubaan-koma-cin-mutuncin-addini-da-malamai-da-shugabanni-ta-hanyar-amfani-da-sabuwar-fasahar-ai-a-duniya-sheikh-sudais/
Ya kara da cewa Mala’iku ma suna gudun wari kamar yadda mutane ke gudunsa.
A matsayin hujja daga Al-Qur’ani, Dr. Bashir ya karanta Suratul A’raf, aya ta 31 wadda ke cewa:
“Yā banī Ādam, khudhū zīnatakum ‘inda kulli masjid…”
Ma’ana: “Ya ‘ya’yan Adamu, ku ɗauki ƙawarku (tsafta da ado) a duk lokacin da za ku je masallaci…”
Ya ce wannan aya karara tana umartar musulmi da su kasance cikin tsabta, tsaftatattun kaya, da siffar mutunci idan za su ziyarci masallaci, musamman a gabar babban ibadar Juma’a.
Dr. Bashir ya kammala da jan kunne cewa rashin tsafta ba wai kawai yana cutar da jama’a ba ne, har ma yana rage darajar sallah, yana kuma hana mutum samun lada cikakke, saboda ya kawo takura ga wasu masu ibada.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/hudubaakwai-tabewa-mutum-ya-rika-yin-sallah-dan-sauke-nauyi-ba-dan-samun-lada-ba-dr-nasir/
Sannan yaja hankalin al’ummar Musulmi da su dage da adu’oin da salatin Annabi Muhammad SAW da karanta suratul Kahafi a duk ranar Juma’a.

