Babban limamin masallacin Juma’a na Masallacin Usman Bn Affan dake Unguwar Gadon Kaya a cikin karamar hukumar Gwale Dr. Aliyu Yunus Muhammad , ya bayyana cewa yawaitar rashin kamun kai da rashin kunya daga wasu mata a wannan zamani na daga cikin alamomin kusantar Tashin Kiyama, kamar yadda Annabi Muhammadu (SAW) ya ambata a cikin hadisai da dama.
Dr. Aliyu Yunus ya bayyana hakan ne yayin gabatar da hudubar sallar Juma’a ta wannan rana 9 ga watan Janairu 2026 , inda ya jaddada cewa Musulunci ya gina al’umma ne bisa kunya,da mutunci da tarbiyya musamman mata , yana mai cewa idan waɗannan suka lalace, to fasadi zai yawaita.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/buduba-cin-amana-da-yaudara-na-daga-cikin-abinda-zai-sa-allah-ya-zare-hannunsa-akan-mutum-ko-waye-farfesa-pantami/
Malamin ya kawo misali da rayuwar Nana A’isha (Radiyallahu Anha) wadda ta nuna muhimmancin kunya a Musulunci.
A cewar riwayoyin hadisi, Nana A’isha ta ce tana shiga ɗakinta inda aka binne Manzon Allah (SAW) da mahaifinta Sayyadina Abu Bakr (RA) ba tare da tsaurara sutura ba, amma bayan da aka binne Sayyadina Umar (RA) a ɗakin, sai ta fara rufe jikinta gaba daya da nuna tsananin kunya, tana cewa:
“Shi Umar mutum ne mai kunya, nakan ji nauyin kasancewa a wurin ba tare da cikakkiyar sutura ba.”
Dr. Aliyu Yunus ya ce wannan hali na Nana A’isha hujja ce bayyananniya da ke nuna matsayin kunya a addinin Musulunci, da kuma yadda Sahabbai da iyalan Annabi (SAW) suka fahimci darajar mutunci da ladabi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubasalon-sunan-gwamnatin-tinubu-na-muslim-muslim-bai-amfanar-da-musulmai-ba-sai-cutar-da-su-dr-aliyu-yunus/
Ya jaddada cewa rashin kunya ba matsalar mata kaɗai ba ce, illa alhakin ya rataya a wuyan kowa da kowa, musamman iyaye, maza,da malamai,da hukumar Hisba da shugabanni da kafafen yaɗa labarai, waɗanda ke da rawar takawa wajen tarbiyyar al’umma.
Malamin ya yi kira ga mata da su ji tsoron Allah su kiyaye mutuncinsu, ga maza kuma da su zama jagorori nagari a gidajensu, tare da jaddada buƙatar komawa ga Alƙur’ani da Sunnah domin gyaran rayuwa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-masu-yada-jita-jita-na-daga-cikin-wadanda-suka-hana-najeriya-zama-lafiya-farfesa-rijiyar-lemo/
Malamin ya kuma nuna takaicinsa kan yadda a yanzu takai ta kawo har Mata ne ke tuka Babur din adaidaita sahu da sanya tufafi na nuna tsiraici a bukukuwan aure da neman gogayya da mata.
Dr. Aliyu Yunus ya kammala da cewa al’umma ba za ta samu tsira ba sai an farfaɗo da kunya da tsoron Allah, domin kunya ginshiƙi ce na imani.

