Fitaccen malamin addinin musulunci kuma limamin masallacin juma’a na Al-Ikilas dake unguwar Sharada Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo, ya bayyana cewa yada jita-jita da samar da labaran ƙarya na daga cikin manyan dalilan da ke ƙara rura wutar rikice-rikice da rashin kwanciyar hankali a Najeriya.
Farfesan ya bayyana hakan ne a hudubarsa ta yau juma’a wanda yace halin da ƙasar nan ke ciki, mutane da yawa na yada bayanai ba tare da tantance gaskiyarsu ba, abin da ya ce na janyo tsoro,da ruɗani, da rashin fahimtar juna a tsakanin al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubamasu-zuwa-sallar-jumaa-ba-tsafta-na-cutar-da-su-kansu-malaiku-dr-bashir-aliyu/
Ya ce wannan dabi’a ta zama wata cibiyar matsala da ke ƙara dagula yanayin tsaro.
“Jita-jita na haddasa fitina a lokuta da dama ,yana tarwatsa al’umma, yana haddasa tashin hankali, da kuma kawo cikas ga zaman lafiya tsakanin yan uwa da maaurata da abokai da manyan mutane Idan ba mu tsaya tsayin daka wajen dakile ta ba, to ba za mu samu ci gaba ba,” in ji Farfesa Rijiyar Lemo.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yadda-jita-jitar-komawar-kwankwaso-apc-ya-janyo-rabuwar-kai-a-apcn-kano/
Ya ƙara da cewa gwamnati,da shugabannin al’umma, da kafafen yaɗa labarai na da rawar gani wajen faɗakar da jama’a kan illolin yaɗa labaran da ba su da tushe, musamman a wannan zamani da kafofin sada zumunta suka mamaye harkokin yau da kullum.
Farfesan ya kuma yi kira ga matasa da su kasance masu kaifin basira wajen tantance bayanai kafin su yada su, domin kada su zama kayan aiki a hannun masu neman tayar da fitina.
Ya jaddada cewa samun zaman lafiya a Najeriya ba wai aikin gwamnati kaɗai ba ne, har ma nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane ɗan ƙasa.

