Babban Malamin Addinin Musulinci dan asalin kasar Burtaniya dake yawan wa’azi a Najeriya Sheikh Muhammad Mahmoud Wanda ya gabatar da hudubar Juma’a a Masallacin Annour da ke Abuja, ya bayyana muhimmancin tsarkake zuciya a rayuwar musulmi, tare da kafa hujjoji daga Al-Kur’ani mai girma.
A hudubar mai taken “Tsarkake Zuciya,” Sheikh Mahmoud ya bayyana cewa zuciya ita ce tushen dukkan ayyukan ɗan Adam, yana mai nuni da ayar da Allah Madaukakin Sarki da ya ce:
Ranar da dukiya da ‘ya’ya ba za su amfana ba. Sai wanda ya zo wa Allah da zuciya mai tsarki.
KARIN LABARAI :https://tsthausa.com/huduba-babu-abin-da-ke-lalata-imani-kamar-shirkashi-ya-sa-hankalinmu-ke-tashi-kanta-dr-kabiru-gombe/
Ya ce wannan aya hujja ce karara da ke nuna cewa tsarkake zuciya ita ce babban abin da zai ceci mutum a ranar Alƙiyama, ba yawan dukiya ko matsayi ba.
Sheikh Muhammad Mahmoud ya kuma ja hankalin jama’a da ayar da Allah ya ce:
Lalle Allah ba ya canza halin da yake a kan wata al’umma har sai sun canza abin da yake cikin zukatansu.
Ya bayyana cewa gyaran al’umma yana farawa ne daga gyaran zuciya, inda ya ce hassada, da ƙiyayya,da munafunci da girman kai suna lalata zuciya tare da janyo fitina da rarrabuwar kai.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-masu-yada-jita-jita-na-daga-cikin-wadanda-suka-hana-najeriya-zama-lafiya-farfesa-rijiyar-lemo/
Haka kuma, ya tunatar da Musulmi da ayar dake cewa
Kuma Ka tsarkake raina, Kai ne mafi alherin Mai tsarkakewa.”
Sheikh ɗin ya ce wannan aya tana nuna cewa samun tsarkakakkiyar zuciya ni’ima ce daga Allah, wadda ake samu ta hanyar gaskiya, tawali’u, yawan ambaton Allah, da kyautata mu’amala da mutane.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubamasu-zuwa-sallar-jumaa-ba-tsafta-na-cutar-da-su-kansu-malaiku-dr-bashir-aliyu/
A ƙarshe, ya yi kira ga al’umma da su dage wajen tsarkake zukatansu ta hanyar yafiya, hakuri da nisantar son zuciya, yana mai cewa hakan ne zai samar da zaman lafiya, hadin kai da albarka a cikin al’umma. Hudubar ta samu halartar dimbin masu ibada da suka cika masallacin Annour domin sauraron wa’azin.

